" />


 

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bukaci bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi a ƙasar su ƙara sanya ido wajen harkokin kasuwanci da mutane daga ƙasashen Kamaru da Croatia da kuma Vietnam.


Matakin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan tsare-tsare da hada-hadar kuɗi Mista Chibuzo Efobi ya fitar a Abuja.


A cewar CBN, bankunan Najeriya da sauran cibiyoyin kudi na bukatar su yi hankali da yin hulɗar kasuwanci da waɗancan ƙasashe, saboda a baya-bayan nan, Hukumar sa ido kan ayyukan halatta kuɗin haram da kuɗaɗen aikata ta'addanci a duniya (FAFT) ta sanya su a jerin ƙasashen da ake sanya wa ido.


Sanarwar ta ce, "An janyo hankalin bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi ga sakamakon da hukumar FAFT ta gudanar daga ranar 21 - 23 ga watan Yuni, 2023 inda ta sanya Kamaru da Croatia da kuma Vietnam a cikin jerin ƙasashe da za a ƙara sa wa ido"


"Bugu da ƙari, Koriya ta Kudu da Iran da Myanmar sun ci gaba da kasancewa cikin jerin ƙasashen da ake sanya wa ido."


A watan Fabrairu, hukumar FAFT dai ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da za a sawa ido amma sanarwar baya-bayan nan daga Hukumar tattara bayanan sirri ta Najeriya ta ce yunkurin da ƙasar ta yi na ficewa daga cikin jerin ya tilastawa FATF rage wuraren da aka ga tana da rauni daga 84 zuwa 15.

Post a Comment

Previous Post Next Post
For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG
ORAIMO OFFICIAL STORE