Babban sakataren hukumar Jin dadin Alhazai ta jihar Kaduna Dr. Yusuf Yakubu Arrigasiyyu, Ya yi kira ga maniya ta aikin hajjin bana a jihar da su qara yawan kudin ajiyarsu zuwa miliyan 2.5 mafi qarancin kudin kujera, kafin ranar 20 February nan da muke ciki.
Dr. Yusuf, yafadi hakan ne a lokacin daya ke ganawa manyan jami'an hukumar da ke kananan hukumomi 23 dake fadin jihar.
Dr. Yusuf, yace hakan zai taimaka wajen turawa hukumar Alhazai ta kasa kudi da wuri domin tabbatar da yawan kujerun da hukumar ta bawa jihar.
Ya kara da cewa a yanzu Hukumar Alhazan ta kasa ta ware wa jihar Kaduna kujeru 5,982 a aikin hajjin bana, Yana mai cewa jihar na bukatan karin kujeru.
Post a Comment