A baya-baya nan ne Majalisar dattawa ta amince da wani kudurin doka da zai ba 'yan siyasa damar tsayawa takara ba tare da jam'iyya ba ko É—an takara mai zaman kansa wato Indifanda.
Ita ma majalisar wakilan Najeriya ta bi sahun majalisar dattawan wajan zartar da kudirin.
Kudirin ya ba 'yan sisaya damar tsayawa takara a matsayin indifanda tun daga matakin kananan hukumomi zuwa na shugaban kasa.
Kudirin dokar ya ba da shawarar cewa duk wani ɗan Najeriya da ya tsaya takarar shugaban kasa a matsayin ɗan takara mai zaman kansa, dole ne ya sami sa hannun akalla kashi 20 na masu zaɓen da aka yi wa rajista daga jihohi 36 na kasar.
Kudirin zai kuma bai wa hukumar zaɓe mai zaman kanta damar tsara biyan kuɗaɗen gudanarwa na 'yan takara masu zaman kansu a zaɓuka daban-daban.
Wasu na ganin cewa kudirin, idan ya zama doka zai taimaka wajan rage danniya ko son zuciyar da ake zargin wasu jam'iyyun siyasa ko shugabannin na nunawa yayin fitar da 'yan takara.
Alhaji Isa Tafida Mafindi wanda jigo ne a harkar siyasar Najeriya ya shaida wa BBC cewa É“angaren kananan hukumomi ne zai fara cin gajiyar kudurin idan ya zama doka
"Wannan kudirin doka idan an sa hannu, farkon ribarsa ga 'yan Najeriya shi ne a matakin kananan hukumomi, don jam'iyya tana tilasta mutane da yawan kuÉ—aÉ—en da za a siya takardar tsayawa takara wanda ba kowa ne zai iya ba" , in ji shi
Dan siyasar ya ce kudirin ba sabon abu ne bane a Najeriya, saboda tsari ne da aka yi amfani da shi a baya: "Lokacinda NPC take da karfi aka yi wa wata jam'iyya da ake kira NEFU ta Malam Aminu Kano, har kuli-kuli da dakuwa mutane suke dorawa don su tabbatar su samu abinda suka sa a cikinsu'".
"Don su isa inda take zuwa ta yi taronta na gaggawa ko jan ra'ayin jama'a kuma kowa zai bada É—an taro, sisi da kobo har jam'iyyar ta ginu".
Dan siyasar ya kuma yi ikirarin cewa tsarin amfani da ɗan takara mai zaman kansa zai taimaka wajan kawarda rigingum addini da na kabilanci saboda 'dan takara ne mai karɓuwa sosai".
Sai dai wani abu da ake ganin zai iya kawo cikas shi ne kurewar lokaci yayinda shugaban kasa mai barin gado ya soma shirye-shiryen miƙa mulki ga zababben shugaban kasa.
Game da haka ne majalisar dattawa ta umurci magatakardar majalisar da ya miƙa wa shugaba Muhammadu Buhari da kudurin doka cikin gaggawa.
Post a Comment