Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya NAHCON, ta ce za ta fara aikin jigilar maniyyata zuwa ƙasa mai tsarki daga ranar Alhamis 25 ga watan Mayu.
Kwamishinan harkokin ma'aikata da kuÉ—i a hukumar, Nura Hassan Yakasai, ya shaida wa BBC cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen wajen fara jigilar mahajjatan bana, inda ya ce alhazan jihar Nasarawa za a fara É—iba a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Ya ce za a kuma kammala kwashe alhazan Najeriya a ranar 18 ga watan Yuni.
Nura Yakasai ya yi kira ga maniyyata da cewa duk wanda aka kira ya tabbata ya fito a kan lokaci domin fara aikin ba tare da samun tsaiko ba.
A ranar Asabar ne alhazan farko daga ƙasashen Malaysia da Bangladesh suka isa Saudiyya domin fara aikin hajjin bana.
Post a Comment