" />


 

Hukumomin ‘yan sandan Najeriya sun sanar da shirin janye wasu jami’an ‘yan sandan da ke ba da kariya da kuma rakiya ga manyan mutane a kasar, da nufin sake tura su aiki a kan tsaron kasa.


Sabon Sufeto-Janar É—in ‘Yan Sandan Najeriya, Olukayode Egbetokun, ya ce, “Duk da cewa kare martabar manyan mutane ya kasance mafi muhimmanci, amma ya zama wajibi mu daidaita abubuwan da muka sa a gaba don magance matsalar tsaro da ke addabar al’ummar Æ™asar baki É—aya.


Wadannan jami’an za a maye gurbinsu ne kawai “inda ya cancanta”, a cewar jaridar Premium Times.


A farkon watan nan ne dai shugaba Bola Tinubu ya yi sauye-sauye a jami'an tsaron Najeriya inda ya nada sabbin kwamandojin jami'an tsaro da suka hada na rundunar sojin ƙasar baki ɗaya.




Post a Comment

Previous Post Next Post
For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG
ORAIMO OFFICIAL STORE