Assalamu Alaikum yan'uwa barka muda sake sadu wa daku a cikin wani sabon darasi kamar yadda kuka gani a sama yau zamu yi bayani akan yadda zaka dawo da duk photo da ka guge a wayar ka
Sau da yawa wasu suna adana hotuna ne domin tarihi, wasu kuma a garesu ba haka bane, wasu suna daukar hotuna su adanasu ne domin hujja ta wani abun, ko kuma shaida ta faruwar wani abun wanda akayi kuma suke tananin za’a iya neman shaida akan faruwar abun, duba da yanayin da rayuwa ta kaimu a halin yanzu na rashin gaskiya da Æ™arancin riÆ™on amana.
A taƙaice dai adana hotuna yana da matuƙar muhimmanci, haka zalika kowa zaiso yaga ya maido da hotunan daya rasa madamar suna da muhimmanci a wajenshi, imma shine ya gogesu da kanshi imma dai wani ne ya goge mashi su.
Kamar yadda muka sani cewa a computer wato na’ura mai Æ™waÆ™walwa akwai wani waje da yake ajiye duk wani abun da aka goge daga cikin computer ‘din har sai anje an goge abun daga can baki ‘daya kafin ya fita duka, wato kamar kwandan shara zamu ce ma wajen, abun yana kasancewa ne kamar yadda muke rayuwarmu ta gida, duk abubuwan da bamaso idan muka tattarasu muna zubasu ne a kwandan shara kafin daga nan mu kwashe su zuwa bola mu zubar, to kafin mukai su bola idan muka tuna mun saka wani abu mai muhimmanci aciki zamu iya dubawa mu ‘dauki abunmu kafin ace mun kaisu bola baki ‘daya.
Itama waya tana da makamancin irin wannan tsarin sai dai nata yasha banban da irin wanda nayi bayani, wato na computer.
Shi wannan wanda zanyi bayani akanshi, wata folder ce mai suna “Thumbnails” ita a 6oye take sai idan an bude wani waje kafin take bayyana.
Amfanin ita wannan folder shine duk wani hoto wanda ya shigo cikin wayarka madamar kayi amfani dashi zata dauki hotonshi ta adana acikin folder ‘din, sai dai kawai bai kai quality ‘din ainihin hoton ba.
Ba iya hoto kadai take dauka ta adana ba, harma video idan ka kalla tana daukar video din hoto kamar irin screenshot ta adana duka acikinta.
Post a Comment