Assalamu Alaikum yan'uwa barka muda kasance wa daku acikin wannan Shafi namu mai Albarka.
Yau juma'a zamuyi bayani akan falalar dake cikin ziyarar mara lafiya ta hanyar kawu muku wasu hadisan manzon Allah (ص) .da kuma adu'ar da akeyi wa mara lafiya.
Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yace duk wanda yazi yarci dan uwan sa wanda (bashi da lafiya) to yana tafiya ne cikin lambun aljannah, Idan kuma ya zauna sai rahama ta yimishi inwa. Idan da safe ne mala'iku dubu saba'in za su yi ta yi ma sa salati harya shiga maraice. Idan kuma da maraice ne mala'iku dubu saba'in za su yi ma sa salati harya sai gari yawa ye.
Imam Tirmizi da ibn majah da Ahmad suka ruwai tushi.
Duba sahih Tirmizi 1/286,da sahih ibn majah 1/244. Haka kuma Ahmad shakir ya inganta shi.
ADU'AR DA AKE WA MARA LAFIYA
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yaka sance Idan ya ziyarci mara lafiya sai ya ce masa:.
لا باس طهور إن شاء الله.
Ma'ana,
Ba komai, tsarkaka ce in Allah ya yarda.
Imam Bukhari ya ruwai tushi.
Duba Sahihul Bukhari da fat'hul Bari 10/118.
2. ا سأل الله العظيم رب العرش العظيم ان يشفيك
Sau 7
Ma'ana, Ina rokon Allah Mai girma, Ubangijin Al'arshi Mai girma, ya baka lafiya.
Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace"Babu wani bawa Musulmi da zai ziyarci mara lafiya wanda ajalinsa bai riga ya zo ba, sannan ya yi wannan Adu'ar sau 7 bakwai face Allah ya bashi lafiya.
Imam Tirmizi da Abu Dawud, suka ruwai tushi,
Duba sahih Tirmizi 2/210, da Sahihul jami'o sagir 5/180
Kada ku manta dayi wa Annabi salati a yau juma'a
Allah shi sa muda ce Amin
Nine naku YUSUF ABUBAKAR
Kuyi share dun wasu su amfana
Nagode.
Allah shi sa muda ce
ReplyDeletePost a Comment